M. Sh 15:7-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. “Idan akwai wani danginku matalauci, a wani gari na cikin garuruwan ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, to, kada ku taurara zuciyarku, ku ƙi sakin hannu ga danginku matalauci.

8. Amma ku ba shi hannu sake, ku ranta masa abin da yake so gwargwadon bukatarsa.

9. Amma fa, ku lura, kada ku yi tunanin banza a zuciyarku, kuna cewa, ‘Ai, shekara ta bakwai, shekarar yafewa ta yi kusa,’ har ku ɗaure wa danginku matalauci fuska, ku ƙi ba shi kome. Zai yi kuka ga Ubangiji a kanku, abin kuwa zai zama laifi a kanku.

10. Sai ku ba shi hannu sake, ba da ɓacin zuciya ba. Saboda wannan Ubangiji zai sa muku albarka cikin aikinku duka, da abin da kuke niyyar yi.

11. Gama ba za a rasa matalauta a ƙasar ba, saboda haka nake umartarku, cewa ku zama da hannu sake ga 'yan'uwanku, da mabukaci, da matalauci.”

12. “Idan aka sayar muku da Ba'ibrane ko mace ko namiji, to, sai ya bauta muku shekara shida, amma a ta bakwai, sai ku 'yantar da shi.

13. Idan kuma kun 'yantar da shi, kada ku bar shi ya tafi hannu wofi.

14. Sai ku ba shi hannu sake daga cikin tumakinku, da awakinku, da masussukar hatsinku, da wurin matsewar inabinku. Ku ba shi kamar yadda Ubangiji Allahnku ya sa muku albarka.

15. Ku tuna dā ku bayi ne a ƙasar Masar, amma Ubangiji Allahnku ya 'yantar da ku, domin haka nake ba ku wannan umarni yau.

16. “Amma idan ya ce muku, ‘Ba na so in rabu da ku,’ saboda yana ƙaunarku da iyalinku, tun da yake yana jin daɗin zama tare da ku,

17. to, sai ku ɗauki basilla ku huda kunnensa har ƙyauren ƙofa, zai zama bawanku har abada. Haka kuma za ku yi da baiwarku.

M. Sh 15