M. Sh 15:10-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Sai ku ba shi hannu sake, ba da ɓacin zuciya ba. Saboda wannan Ubangiji zai sa muku albarka cikin aikinku duka, da abin da kuke niyyar yi.

11. Gama ba za a rasa matalauta a ƙasar ba, saboda haka nake umartarku, cewa ku zama da hannu sake ga 'yan'uwanku, da mabukaci, da matalauci.”

12. “Idan aka sayar muku da Ba'ibrane ko mace ko namiji, to, sai ya bauta muku shekara shida, amma a ta bakwai, sai ku 'yantar da shi.

13. Idan kuma kun 'yantar da shi, kada ku bar shi ya tafi hannu wofi.

14. Sai ku ba shi hannu sake daga cikin tumakinku, da awakinku, da masussukar hatsinku, da wurin matsewar inabinku. Ku ba shi kamar yadda Ubangiji Allahnku ya sa muku albarka.

15. Ku tuna dā ku bayi ne a ƙasar Masar, amma Ubangiji Allahnku ya 'yantar da ku, domin haka nake ba ku wannan umarni yau.

16. “Amma idan ya ce muku, ‘Ba na so in rabu da ku,’ saboda yana ƙaunarku da iyalinku, tun da yake yana jin daɗin zama tare da ku,

17. to, sai ku ɗauki basilla ku huda kunnensa har ƙyauren ƙofa, zai zama bawanku har abada. Haka kuma za ku yi da baiwarku.

18. Sa'ad da kuka 'yantar da shi kada ku damu, gama shekara shida ya yi muku bauta wadda ta ninka ta ɗan ƙodago. Ubangiji Allahnku kuwa zai sa muku albarka cikin dukan abin da kuke yi.”

19. “Sai ku keɓe wa Ubangiji Allahnku dukan 'yan fari maza waɗanda aka haifa muku daga cikin garkenku na shanu, da na tumaki, da na awaki. Kada ku yi aiki da ɗan farin shanunku, kada kuma ku sausayi ɗan farin tunkiyarku.

20. Ku da iyalanku za ku ci shi kowace shekara a gaban Ubangiji Allahnku a wurin da Ubangiji zai zaɓa.

21. Idan yana da wani lahani kamar gurguntaka ko makanta, ko kowane irin mugun lahani, to, kada ku miƙa shi hadaya ga Ubangiji Allahnku.

M. Sh 15