M. Sh 13:11-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Da haka nan dukan Isra'ilawa za su ji, su ji tsoro, har da ba za su ƙara aikata mugun abu irin wannan a cikinku ba.

12-13. “Idan kuka ji akwai 'yan ashararu a wani gari wanda Ubangiji Allahnku ya ba ku ku zauna a ciki, sun fito daga cikinku, suka rikitar da mazaunan garin suna cewa, ‘Ku zo mu bauta wa gumaka,’ waɗanda ba ku san su ba,

14. to, sai ku bincike labarin sosai a hankali. Idan hakika gaskiya ne, mugun abu haka ya faru a cikinku,

15. sai ku karkashe dukan mazaunan garin da takobi, ku kuma karkashe dabbobin da suke cikinsa. Za ku hallaka garin ƙaƙaf.

16. Ku tattara dukan ganimar garin a dandali, ku ƙone garin da dukan ganimar, hadaya ta ƙonawa ce ga Ubangiji Allahnku. Garin zai zama kufai har abada, ba za a ƙara gina shi ba.

17. Kada ku ɗauka daga cikin abin da aka haramta don zafin fushin Ubangiji ya huce, ya yi muku jinƙai, ya ji tausayinku, ya kuma riɓaɓɓanya ku ma kamar yadda ya rantse wa kakanninku,

18. in dai za ku yi wa Ubangiji Allahnku biyayya, ku kiyaye dukan umarnansa waɗanda nake umartarku da su yau, ku kuma ku aikata abin da yake daidai ga Ubangiji Allahnku.”

M. Sh 13