29. “Sai na ce muku, ‘Kada ku ji tsoronsu ko ku firgita.
30. Ubangiji Allahnku wanda yake tafiya tare da ku, shi kansa zai yi yaƙi dominku kamar yadda ya yi muku a Masar a kan idonku.
31. Kun ma ga yadda Ubangiji ya bi da ku cikin jeji kamar yadda mutum yakan bi da ɗansa, a dukan tafiyarku har zuwa wannan wuri.’
32. Amma ko da yake ya yi muku haka duk da haka ba ku dogara ga Ubangiji Allahnku ba.
33. Shi wanda ya bishe ku, ya nuna muku inda za ku yi zango. Da dare yakan nuna muku hanya da wuta, da rana kuma yakan bi da ku da girgije.”
34. “Ubangiji kuwa ya ji maganganunku, sai ya yi fushi, ya rantse, ya ce,
35. ‘Daga cikin mutanen wannan muguwar tsara ba wanda zai ga ƙasan nan mai albarka wadda na rantse zan ba kakanninku,
36. sai dai Kalibu ɗan Yefunne, shi kaɗai ne zai gan ta. Zan ba shi da 'ya'yansa ƙasar da ƙafarsa ta taka, gama shi ne ya bi Ubangiji sosai.’
37. Ubangiji ma ya yi fushi da ni sabili da ku, ya ce, ‘Har kai ma ba za ka shiga ba.
38. Baranka, Joshuwa ɗan Nun, shi ne zai shiga. Sai ka ƙarfafa masa zuciya gama shi ne zai bi da Isra'ilawa, har su amshi ƙasar, su gaje ta.’
39. “Sa'an nan Ubangiji ya ce wa dukanmu, ‘Amma 'ya'yanku ƙanana waɗanda ba su san mugunta ko nagarta ba, waɗanda kuke tsammani za a kwashe su ganima, su ne za su shiga ƙasar. Ni Ubangiji zan ba su su mallake ta.
40. Amma ku, sai ku koma cikin jeji ta hanyar Bahar Maliya.’ ”
41. “Sa'an nan kuka amsa mini, kuka ce, ‘Mun yi wa Ubangiji Allahnmu zunubi. Za mu tafi mu yi yaƙi bisa ga faɗar Ubangiji Allahnmu.’ Sai kowannenku ya yi ɗamara ya ɗauki makaman yaƙinsa, kuka yi tsammani abu mai sauƙi ne ku shiga ƙasar tuddai.