M. Had 2:11-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Na yi tunani a kan dukan abin da na aikata, da irin wahalar da na sha lokacin da nake yin aikin, sai na gane ba shi da wata ma'ana, na zama kamar mai harbin iska, ba shi da wani amfani.

12. Bayan wannan duka, abin da sarki zai iya yi kaɗai, shi ne abin da sarakunan da suka riga shi suka yi.Sai na fara tunani a kan abin da ake nufi da hikima, ko rashin kula, ko wauta.

13. To, na sani hikima ta fi wauta, kamar yadda haske ya fi duhu.

14. Mai hikima ya san inda ya nufa, amma wawa ba zai iya sani ba. Na kuma sani makomarsu guda ce.

15. A zuciyata na ce, “Abin da yakan sami wawa shi ne kuma zai same ni. To, wace riba na ci ke nan saboda hikimar da nake da ita?” Na kuma ce a zuciyata, “Wannan ma aikin banza ne.”

16. Gama ba za a ƙara tunawa da mai hikima ko wawa ba, nan gaba za a manta da dukansu. Yadda mai hikima yake mutuwa haka ma wawa yake mutuwa.

17. Saboda haka rai ba wani abu ba ne a gare ni, domin dukan abin da yake cikinsa bai kawo mini kome ba sai wahala. Duka banza ne, ba abin da nake yi sai harbin iska kawai.

18. Daga cikin dukan abin da na samu kan aikin da na yi, ba su da wata ma'ana a gare ni, gama na sani zan bar wa magājina ne.

19. Wa ya sani ko shi mai hikima ne, ko kuma wawa ne? Duk da haka shi zai mallaki dukan abin da na sha wahalar tanadinsa. Dukan aikin da na yi na hikima a wannan duniya aikin banza ne.

20. Na yi baƙin ciki a kan dukan wahalar aikin da na yi a duniya.

21. Kai ne ka yi aiki da dukan hikimarka, da iliminka, da gwanintarka, amma kuma tilas ka bar shi duka ga wanda bai yi wahalar kome a ciki ba. Wannan ma bai amfana kome ba, mugun abu ne.

22. Me mutum zai samu daga cikin aikin da ya yi duka, da irin ɗawainiyar da ya sha a kan yin aikin?

M. Had 2