1. Mutanen Ifraimu suka yi gangami suka haye zuwa Zafon da shirin yaƙi. Suka ce wa Yefta, “Me ya sa ka haye zuwa yaƙi da Ammonawa, amma ba ka kira mu mu tafi tare da kai ba? To, yanzu za mu ƙone ka da gidanka.”
2. Amma Yefta ya amsa musu, ya ce, “Ni da mutanena mun yi ta jayayya da Ammonawa, na kira ku don ku cece ni, amma ba ku cece ni daga hannunsu ba.
3. Sa'ad da na ga ba ku cece ni ba, sai na yi kasai da raina, na haye don in yi karo da Ammonawa. Ubangiji kuwa ya ba da su a hannuna. Me ya sa kuka zo yau don ku yi yaƙi da ni?”