L. Kid 4:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya faɗa wa Musa da Haruna,

2. su ƙidaya 'ya'yan Kohat, maza, daga cikin 'ya'yan Lawi bisa ga iyalansu da gidajen kakanninsu,

3. su ƙidaya daga mai shekara talatin zuwa hamsin, wato waɗanda suka isa su yi aiki a alfarwa ta sujada.

4. Wannan shi ne aikin 'ya'yan Kohat, maza, a cikin alfarwa ta sujada a kan abubuwa mafi tsarki.

5. Sa'ad da za a tashi daga zango, sai Haruna, tare da 'ya'yansa maza, su shiga cikin alfarwa, su kwance labulen kāriya, su rufe akwatin alkawari da shi.

6. Sa'an nan kuma su rufe shi da fatun awaki, su kuma shimfiɗa shuɗin zane a bisansa, su zura masa sandunansa.

7. Sai su shimfiɗa shuɗin zane a kan tebur na gurasar ajiyewa, sa'an nan su dībiya farantai, da cokula, da kwanonin, da butocin hadaya ta sha, da gurasar ajiyewa.

8. Sa'an nan su rufe su da jan zane, a kuma rufe su da fatun awaki, sa'an nan su zura masa sandunansa.

9. Su kuma ɗauki shuɗin zane su rufe alkuki, da fitilunsa, da hantsukansa, da farantansa, da dukan kwanonin man da akan zuba masa.

34-48. Musa da Haruna da shugabannin taron jama'a kuwa suka ƙidaya iyalan Lawiyawa uku, wato Kohatawa, da Gershonawa da Merariyawa bisa ga iyalansu da gidajen kakanninsu, aka rubuta dukan mazaje daga mai shekara talatin zuwa mai shekara hamsin, waɗanda za su iya aiki a alfarwa ta sujada, kamar haka, Kohat dubu biyu da ɗari bakwai da hamsin (2,750), Gershon dubu biyu da ɗari shida da talatin (2,630), Merari dubu uku da ɗari biyu (3,200), Jimilla duka, dubu takwas da ɗari biyar da tamanin (8,580).

L. Kid 4