L. Kid 35:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A filayen Mowab a wajen Urdun daura da Yariko, Ubangiji ya yi magana da Musa, ya ce,

2. “Ka umarci jama'ar Isra'ila, ka ce su ba Lawiyawa biranen da za su zauna a ciki daga cikin gādonsu, za su kuma ba Lawiyawa hurumi kewaye da biranen.

3. Biranen za su zama nasu, inda za su zauna, hurumi kuwa domin shanunsu da sauran dukan dabbobinsu.

4. Girman hurumin da za su ba Lawiyawa kewaye da biranen zai zama mai fāɗin kamu dubu kewaye da garun birnin.

5. A bayan birnin za a auna kamu dubu biyu a wajen gabas, kamu dubu biyu a wajen kudu, kamu dubu biyu a wajen yamma, kamu dubu biyu a wajen arewa. Wannan zai zama hurumin mutanen birnin. Birnin kuwa zai kasance a tsakiya.

6. A cikin biranen da za a ba Lawiyawa, shida su zama na mafaka, inda za a yarda wa mai kisankai ya gudu zuwa can. Banda biranen mafaka guda shida, za a kuma ba su birane arba'in da biyu.

7. Wato dukan biranen da za a ba Lawiyawa guda arba'in da takwas ne tare da huruminsu.

L. Kid 35