L. Kid 31:26-37 Littafi Mai Tsarki (HAU)

26. “Da kai, da Ele'azara firist, da shugabannin gidajen kakannin taron jama'a, ku lasafta yawan mutane, da dabbobin da aka kwaso ganima.

27. Ku kasa ganima kashi biyu, ku ba sojojin da suka tafi yaƙi kashi ɗaya, kashi ɗayan kuwa ku ba taron jama'ar.

28. Sai ka karɓi na Ubangiji daga cikin kashin ganimar da aka baiwa sojojin da suka tafi yaƙi. Ka ɗauki ɗaya daga cikin mutum ɗari biyar, da shanu ɗari biyar, da jakai ɗari biyar, da tumaki ɗari biyar.

29. Ka ba Ele'azara firist. Wannan hadaya ta ɗagawa ce ga Ubangiji.

30. Daga cikin rabin ganimar da aka ba Isra'ilawa, sai ka ɗauki ɗaya ɗaya daga cikin mutum hamsin, da shanu hamsin,da jakai hamsin, da tumaki hamsin, da dukan dabbobin. Ka ba da su ga Lawiyawa waɗanda suke lura da alfarwar sujada ta Ubangiji.”

31. Musa da Ele'azara firist, suka yi yadda Ubangiji ya umarci Musa.

32. Yawan ganimar da sojoji suka kawo ke nan, tumaki dubu ɗari shida da dubu saba'in da dubu biyar (675,000),

33. shanu dubu saba'in da dubu biyu (72,000),

34. jakai dubu sittin da dubu ɗaya (61,000),

35. 'yan mata dubu talatin da dubu biyu (32,000) waɗanda ba su san namiji ba.

36. Kashin da aka ba sojoji waɗanda suka tafi yaƙi ne nan, tumaki dubu ɗari uku da talatin da bakwai da ɗari biyar (337,500).

37. Daga ciki aka fitar da tumaki ɗari shida da saba'in da biyar domin Ubangiji.

L. Kid 31