21. Ele'azara firist kuwa, ya ce wa sojojin da suka tafi yaƙi, “Waɗannan su ne ka'idodin da Ubangiji ya ba Musa.
22. Zinariya, da azurfa, da tagulla, da baƙin ƙarfe, da kuza, da darma,
23. da dukan abin da wuta ba ta ci ba, su ne za ku tsarkake su da wutar tsarkakewa, duk da haka za a kuma tsarkake shi da ruwa. Amma abin da wuta takan ci, sai a tsarkake shi da ruwa kawai.
24. Ku wanke tufafinku a rana ta bakwai don ku tsarkaka, bayan haka ku shiga zangon.”
25. Ubangiji kuma ya ce wa Musa,
26. “Da kai, da Ele'azara firist, da shugabannin gidajen kakannin taron jama'a, ku lasafta yawan mutane, da dabbobin da aka kwaso ganima.
27. Ku kasa ganima kashi biyu, ku ba sojojin da suka tafi yaƙi kashi ɗaya, kashi ɗayan kuwa ku ba taron jama'ar.
28. Sai ka karɓi na Ubangiji daga cikin kashin ganimar da aka baiwa sojojin da suka tafi yaƙi. Ka ɗauki ɗaya daga cikin mutum ɗari biyar, da shanu ɗari biyar, da jakai ɗari biyar, da tumaki ɗari biyar.
29. Ka ba Ele'azara firist. Wannan hadaya ta ɗagawa ce ga Ubangiji.
30. Daga cikin rabin ganimar da aka ba Isra'ilawa, sai ka ɗauki ɗaya ɗaya daga cikin mutum hamsin, da shanu hamsin,da jakai hamsin, da tumaki hamsin, da dukan dabbobin. Ka ba da su ga Lawiyawa waɗanda suke lura da alfarwar sujada ta Ubangiji.”