L. Kid 25:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sa'ad da Isra'ilawa suka yi zango a Shittim, maza suka fara yin lalata da matan Mowabawa.

2. Waɗannan mata sukan gayyaci mutanen zuwa wajen shagalin tsafinsu. Isra'ilawa kuwa sukan ci abinci, su kuma yi sujada ga gumaka.

3. Ta haka Isra'ilawa suka shiga bautar gumakan Ba'al na Feyor. Sai Ubangiji ya husata da Isra'ilawa.

4. Ya ce wa Musa, “Ɗauki sugabannin jama'a, ka rataye su a rana a gabana don in huce daga fushin da nake yi da Isra'ilawa.”

L. Kid 25