L. Kid 21:25-33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

25. Isra'ilawa kuwa suka ci dukan waɗannan birane, suka zauna a biranen Amoriyawa, wato a Heshbon da ƙauyukanta duka.

26. Gama Heshbon ita ce birnin Sihon,Sarkin Amoriyawa, wanda ya yi yaƙi da Sarkin Mowab na dā. Ya ƙwace ƙasarsa duka daga hannunsa har zuwa Kogin Arnon.

27. Domin haka mawaƙa sukan ce,“Ku zo Heshbon, bārin sarki Sihon!Muna so mu ga an sāke gina an kuma fanso shi.

28. Gama sojojin Sihon sun shiga kamar wuta,A wannan birni na Heshbon,Sun cinye Ar ta Mowab,Ta murƙushe tuddan Arnon.

29. Kaitonku, ku mutanen Mowab!Ku masu sujada ga Kemosh kun lalace!Gumakanku sun sa mutane su zama 'yan gudun hijira,Mata kuwa, Sihon, Sarkin Amoriyawa ya kama su.

30. Amma yanzu an hallaka zuriyarsu,Tun daga Heshbon har zuwa Dibon,Har da Nofa kusa da Medeba.”

31. Haka fa Isra'ilawa suka zauna a ƙasar Amoriyawa.

32. Sai Musa ya aika a leƙo asirin ƙasar Yazar. Suka tafi suka ci ƙauyukanta, suka kori Amoriyawan da suke can.

33. Suka juya suka haura ta hanyar Bashan. Sai Og, Sarkin Bashan, da dukan jama'arsa suka fita, suka yi yaƙi da su a Edirai.

L. Kid 21