L. Kid 16:19-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. Sai Kora ya tara dukan taron jama'a a bakin alfarwa ta sujada, ya zuga su su tayar wa Musa, da Haruna. Sai ɗaukakar Ubangiji ta bayyana ga dukan taron jama'ar.

20. Ubangiji kuwa ya ce wa Musa da Haruna,

21. “Ku ware kanku daga cikin taron jama'ar nan, ni kuwa in hallaka su nan take.”

22. Sai Musa da Haruna suka fāɗi rubda ciki, suka ce, “Ya Allah, Allahn ruhohin 'yan adam duka, za ka yi fushi da dukan taron jama'a saboda zunubin mutum ɗaya?”

23. Sai Ubangiji ya ce wa Musa,

24. “Ka faɗa wa jama'a su tashi, su nisanci alfarwar Kora, da ta Datan, da ta Abiram.”

25. Musa kuwa ya tashi ya tafi wurin Datan, da Abiram Dattawan Isra'ilawa suka bi Musa.

26. Sai ya ce wa jama'ar, “Ina roƙonku, ku ƙaurace wa alfarwan waɗannan mugayen mutane, kada ku taɓa kowane abu da yake nasu, domin kada a shafe ku saboda zunubansu.”

27. Sai jama'a suka tashi daga inda Kora, da Datan, da Abiram suke zama.Datan da Abiram kuwa suka fito suka tsaya a ƙofar alfarwansu tare da matansu da 'ya'yansu, da 'yan ƙananansu.

L. Kid 16