L. Kid 15:3-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Sa'ad da za su yi hadayar da akan yi da wuta ga Ubangiji daga cikin garken shanu, ko na tumaki da awaki, ko hadaya ta ƙonawa ce, ko ta cika wa'adi ce, ko ta yardar rai ce, ko ta ƙayyadaddun idodinsu ce, don a ba da ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji,

4. sai shi wanda ya kawo hadayar ga Ubangiji, ya kuma kawo hadaya ta gari, humushin garwa guda kwaɓaɓɓe da rubu'in moɗa na mai.

5. Ya kuma shirya hadaya ta sha, rubu'in moɗa ta ruwan inabi domin kowane ɗan rago na hadaya ta ƙonawa.

6. Idan kuwa da rago ne, a shirya hadaya ta gari humushi biyu na garwa, a kwaɓa da sulusin moɗa na mai.

7. Za a kuma miƙa hadaya ta sha da sulusin moɗa na ruwan inabi, don a yi ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji.

8. Idan kuwa da bijimi ne za a yi hadaya ta ƙonawar, ko sadaka domin cika wa'adi, ko ta salama ga Ubangiji,

9. sai a miƙa hadaya ta gari tare da bijimin, humushi uku na garwar gari kwaɓaɓɓe da rabin moɗa na mai.

10. Za a kuma miƙa hadaya ta sha da rabin moɗa na ruwan inabi. Hadaya ce da akan yi da wuta, mai yin ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji.

11. Haka za a yi da kowane bijimi, ko rago,ko ɗan rago,ko bunsuru.

12. Bisa ga yawan abin da aka shirya, haka za a yi da kowannensu bisa ga adadinsu.

13. Haka dukan waɗanda suke 'yan ƙasa za su yi in za su ba da hadayar da akan yi da wuta don yin ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji.

14. Idan baƙon da yake baƙunci a cikinsu ko ko wane ne da yake tare da su a dukan zamanansu, yana so ya ba da hadayar da akan yi da wuta don a yi ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji, sai ya yi kamar yadda suke yi.

15. Ka'ida ɗaya ce domin taron jama'a da kuma baƙin da yake zaune tare da su. Ka'ida ce madawwamiya a dukan zamanansu. Kamar yadda suke a gaban Ubangiji, haka kuma baƙon da yake baƙunci a cikinsu yake.

16. Ka'ida ɗaya ce umarni kuma ɗaya ne domin su da baƙin da yake baƙunci a cikinsu.

L. Kid 15