L. Kid 15:23-35 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. wato duk dai abin da ubangiji ya umarta ta bakin Musa tun daga ranar da Ubangiji ya ba da umarnan, har zuwa dukan zamanansu,

24. idan jama'a sun yi kuskure da rashin sani, sai su miƙa maraƙi don yin hadaya ta ƙonawa don a yi ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji. Su kuma ba da hadaya ta gari, da hadaya ta sha tare da maraƙin bisa ga ka'idar. Za su kuma miƙa bunsuru ɗaya na yin hadaya don zunubi.

25. Firist kuwa zai yi kafara domin dukan jama'ar Isra'ilawa, za a kuwa gafarta musu kuskuren, domin sun kawo hadaya ta ƙonawa da hadaya don zunubi ga Ubangiji saboda kuskurensu.

26. Za a gafarta wa dukan taron jama'ar Isra'ilawa da baƙon da yake baƙunci a cikinsu, kuskuren da suka yi.

27. Idan bisa ga kuskure wani mutum ya yi zunubi, sai ya ba da 'yar akuya bana ɗaya ta yin hadaya don zunubi.

28. Firist kuwa zai yi kafara a gaban Ubangiji saboda mutumin da ya yi kuskuren, gama ya yi zunubi ba da saninsa ba, za a kuwa gafarta masa.

29. Ka'idarsu ɗaya ce a kan wanda ya yi kuskure, ko Ba'isra'ile ne, ko baƙon da yake baƙunci a cikinsu.

30. Amma mutumin da ya yi laifi da gangan, ko shi ɗan ƙasa ne, ko kuma baƙo ne, ya sāɓi Ubangiji, sai a kashe shi,

31. gama ya raina maganar Ubangiji, ya karya umarninsa. Hakika za a kashe mutumin nan, alhakin zunubinsa, yana wuyansa.

32. Sa'ad da Isra'ilawa suke jeji, sai aka iske wani yana tattara itace a ranar Asabar.

33. Sai suka kai shi wurin Musa, da Haruna, da dukan taron jama'a.

34. Aka sa shi a gidan waƙafi domin ba a bayyana abin da za a yi da shi ba tukuna.

35. Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “A kashe mutumin, dukan taron jama'a za su jajjefe shi da duwatsu a bayan zangon.”

L. Kid 15