L. Kid 14:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sai dukan taron jama'a suka yi kuka da babbar murya dukan dare saboda wahala.

2. Dukan Isra'ilawa suka yi gunaguni a kan Musa da Haruna, suke ce, “Da ma mun mutu a ƙasar Masar, ko kuwa a wannan jeji.

3. Me ya sa Ubangiji ya kawo mu a wannan ƙasa, mu mutu da takobi? Matanmu da ƙanananmu za su zama ganima. Ba zai fi mana kyau, mu koma Masar ba?”

4. Sai suka ce wa juna, “Bari mu shugabantar da wani, mu koma Masar.”

5. Sa'an nan Musa da Haruna suka fāɗi rubda ciki a gaban dukan taron jama'ar Isra'ilawa.

L. Kid 14