L. Kid 10:30-36 Littafi Mai Tsarki (HAU)

30. Amma ya ce masa, “Ba zan tafi ba, zan koma ƙasata da wurin dangina.”

31. Musa kuwa ya ce masa, “Ina roƙonka kada ka rabu da mu, gama ka san jejin da muke zango, kai za ka zama idonmu.

32. Idan ka tafi tare da mu, kowane irin alheri da Ubangiji zai yi mana, mu kuma haka za mu yi maka.”

33. Sai suka tashi daga dutsen Ubangiji, wato Sinai, suka yi tafiya kwana uku. Akwatin alkawarin Ubangiji kuwa ya wuce gabansu don ya nemar musu masauki.

34. A duk lokacin da suka tashi daga zango, sai girgijen Ubangiji ya inuwantar da su da rana.

35. Duk kuma lokacin da akwatin zai tashi, sai Musa ya ce, “Ka tashi, ya Ubangiji, ka sa maƙiyanka su warwatse, ka sa waɗanda suke ƙinka su gudu gabanka.”

36. Sa'ad da akwatin ya sauka kuma, Musa yakan ce, “Ka komo, ya Ubangiji, a wurin dubun dubbai na iyalan Isra'ila.”

L. Kid 10