10. A ranar murnarku, da lokacin ƙayyadaddun idodinku, da tsayawar watanninku, za ku busa kakakin a lokacin yin hadayunku na ƙonawa, da hadayunku na salama. Za su zama sanadin tunawa da ku a gaban Allahnku. Ni ne Ubangiji Allahnku.”
11. A rana ta ashirin ga watan biyu a shekara ta biyu, sai aka gusar da girgijen daga kan alfarwa ta sujada.
12. Isra'ilawa kuwa suka tashi daki-daki daga jejin Sinai. Girgijen kuma ya tsaya a jejin Faran.
13. Suka fara tafiyarsu bisa ga umarnin da Ubangiji ya yi wa Musa.
14. Tutar zangon kabilar mutanen Yahuza ta fara tashi, ƙungiyoyinsu suna biye. Nashon, ɗan Amminadab, shi ne shugaban rundunarsu.
15. Shugaban rundunar kabilar mutanen Issaka Netanel ne, ɗan Zuwar.
16. Shugaban rundunar kabilar mutanen Zabaluna Eliyab ne, ɗan Helon.
17. Sa'an nan aka kwankwance alfarwar, sai 'ya'yan Gershon, da 'ya'yan Merari masu ɗaukar alfarwar suka kama hanya.
18. Tutar zangon kabilar mutanen Ra'ubainu ta tashi, ƙungiyoyinsu suna biye. Shugaban rundunarsu Elizur ne, ɗan Shedeyur.
19. Shugaban rundunar kabilar mutanen Saminu kuwa Shelumiyel ne, ɗan Zurishaddai.