21. Za a shirya shi da mai a kwanon tuya. A kwaɓa shi sosai, a toya shi dunƙule dunƙule kamar hadaya ta gari, sa'an nan a kawo shi a miƙa shi don ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji.
22. Wanda aka keɓe daga zuriyar Haruna, shi ne zai miƙa wannan hadaya ga Ubangiji. Za a ƙone ta duka. Wannan farilla ce har abada.
23. Kowace hadaya ta gari ta firist, za a ƙone ta ɗungum, ba za a ci ba.
24. Sai Ubangiji ya umarci Musa
25. ya ba Haruna da 'ya'yansa maza waɗannan ka'idodi domin hadaya don zunubi. A inda ake yanka hadaya ta ƙonawa, a nan ne za a yanka hadaya don zunubi a gaban Ubangiji, hadaya ce mai tsarki.
26. Firist wanda ya miƙa hadaya don zunubi zai ci daga ciki a wuri mai tsarki a cikin farfajiyar alfarwa ta sujada.
27. Duk wanda ya taɓa naman zai tsarkaka, in kuma jinin ya ɗiga a riga, sai a wanke rigar a wuri mai tsarki.
28. Sai a fasa tukunyar ƙasa wadda aka dafa naman a ciki, amma in a cikin tukunyar tagulla aka dafa, sai a kankare ta a ɗauraye da ruwa.
29. Kowane namiji a cikin firistoci zai iya cin naman, gama abu ne mafi tsarki.
30. Amma ba za a ci naman hadaya don zunubi ba wanda aka shigar da jininsa a alfarwa ta sujada domin yin kafara a Wuri Mai Tsarki. Sai a ƙone shi da wuta.