L. Fir 26:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya ce, “Kada ku yi wa kanku gumaka, ko ku kafa sassaƙaƙƙiyar siffa, ko al'amudi. Kada kuma ku kafa wata siffa ta dutse a ƙasarku da za ku durƙusa mata, gama ni ne Ubangiji Allahnku.

2. Sai ku kiyaye lokatan sujadata, ku girmama alfarwa ta sujada. Ni ne Ubangiji.

3. “Idan kun bi dokokina, kun kiyaye umarnaina, kun aikata su,

4. sa'an nan zan ba da ruwan sama a lokacinsa, ƙasar kuwa za ta ba da albarkarta, itatuwan gonaki kuma za su ba da 'ya'yansu.

5. Za ku yi ta girbi, har lokacin tattara 'ya'yan inabi, za ku kuma yi ta tattara 'ya'yan inabi har zuwa lokacin shuka. Za ku ci abincinku, ku ƙoshi, ku yi zamanku a ƙasarku lafiya.

6. “Zan ba da salama cikin ƙasar. Za ku kwanta, ba abin da zai razana ku. Zan kawar da mugayen dabbobi daga ƙasar. Ba za a ƙara yin yaƙi a ƙasarku ba.

7. Za ku runtumi maƙiyanku, za su kuwa fāɗi ta kaifin takobi a gabanku.

8. Mutum biyar ɗinku za su runtumi mutum ɗari, mutum ɗari ɗinku za su runtumi mutum dubu goma. Maƙiyanku kuwa za su fāɗi a gabanku ta kaifin takobi.

L. Fir 26