16. Da haka zai yi kafara domin Wuri Mai Tsarki saboda ƙazantar mutanen Isra'ila, da laifofinsu, da dukan zunubansu. Haka kuma zai yi wa alfarwa ta sujada, wadda take a wurinsu, a tsakiyar ƙazantarsu.
17. Kada kowa ya kasance cikin alfarwar sujada lokacin da Haruna ya shiga Wuri Mafi Tsarki domin ya yi kafara don kansa, da gidansa, da dukan taron jama'ar Isra'ila, sai lokacin da ya fita.
18. Sa'an nan zai fita ya tafi wurin bagade wanda yake gaban Ubangiji don ya yi kafara dominsa. Zai ɗibi jinin bijimin da na bunsurun, ya shafa wa zankayen bagaden a kewaye.