7. Sa'an nan 'ya'yan Haruna maza, firistoci, za su hura wuta a bisa bagaden, su jera itace daidai a wutar.
8. Su ɗibiya gunduwoyin, da kan, da kitsen bisa itacen da yake cikin wutar da take a kan bagaden.
9. Amma mai hadayar zai wanke kayan ciki da ƙafafu da ruwa, sa'an nan firist ya ƙone duka a kan bagaden, hadaya ce ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
10. Idan hadayarsa ta ƙonawa daga cikin garken tumaki ko kuwa na awaki ne, sai ya ba da namiji marar lahani.
11. Zai yanka shi a arewacin bagaden a gaban Ubangiji. 'Ya'yan Haruna, firistoci, za su yayyafa jinin a kewaye da bagaden.
12. Mai hadayar kuma zai yanyanka shi gunduwa-gunduwa, da kansa, da kitsensa. Firist zai jera su a bisa itacen da yake cikin wutar da take a bagaden.
13. Amma mai hadayar zai wanke kayan ciki da ƙafafu da ruwa, sa'an nan firist ya miƙa duka, ya ƙone a bisa bagaden, gama hadaya ce ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.