11. Zai yanka shi a arewacin bagaden a gaban Ubangiji. 'Ya'yan Haruna, firistoci, za su yayyafa jinin a kewaye da bagaden.
12. Mai hadayar kuma zai yanyanka shi gunduwa-gunduwa, da kansa, da kitsensa. Firist zai jera su a bisa itacen da yake cikin wutar da take a bagaden.
13. Amma mai hadayar zai wanke kayan ciki da ƙafafu da ruwa, sa'an nan firist ya miƙa duka, ya ƙone a bisa bagaden, gama hadaya ce ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
14. Idan kuma hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji daga cikin tsuntsaye ne, sai ya kawo kurciyoyi, ko 'yan tattabarai.