1. To, ina so ku san irin yawan shan faman da nake yi dominku, da waɗanda suke a Lawudikiya, da kuma duk waɗanda ba su taɓa ganina ba.
2. Sona a ƙarfafa musu zuciya, ƙauna tana haɗa su, har su sami dukkan mayalwaciyar fahimta tabbatacciya, da sanin asirin nan na Allah, wato Almasihu,
3. wanda shi ne taska, wato maɓoyar dukkan mafifitan hikima da sani.
4. Na faɗi wannan ne don kada kowa ya hilace ku da maganar yaudara.
5. Don ko da yake a jiki ba na nan, ai, ruhuna yana nan tare da ku, ina kuwa farin cikin ganin kyakkyawan tsarinku, da dagewarku a kan bangaskiyarku ga Almasihu.
6. Da yake kun yi na'am da Almasihu Yesu Ubangiji, to, sai ku tsaya a gare shi,
7. kuna kafaffu, kuna ginuwa a cikinsa, kuna tsayawa da bangaskiya gaba gaba, daidai yadda aka koya muku, kuna gode wa Allah a koyaushe.
8. Ku lura fa, kada kowa ya ribace ku ta hanyar iliminsa na yaudarar wofi, bisa ga al'adar mutane kawai, wato, bisa ga al'adun duniyar nan, ba bisa ga koyarwar Almasihu ba.
9. Domin a cikinsa ne cikin jiki dukkan cikar Allahntaka take tabbata.
10. A gare shi ne aka kammala ku, wanda yake shi ne shugaban dukkan sarauta da iko.
11. A cikinsa ne kuma aka yi muku kaciya, ba kuwa yin mutum ba, amma wadda Almasihu ya yi muku ce, ta wurin tuɓe halinku na mutuntaka.
12. An kuma binne ku tare da shi a wajen baftisma, inda kuma aka tashe ku tare da shi saboda bangaskiyarku ga ikon Allah, wanda ya tashe shi daga matattu.
13. Ku kuma da kuke matattu saboda laifofinku, marasa kaciya ta jiki, Allah ya raya ku tare da Almasihu, ya yafe mana dukkan laifofinmu,