K. Mag 15:8-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Ubangiji yana murna sa'ad da adalai suke yin addu'a, amma yana ƙin hadayun da mugaye suke miƙa masa.

9. Ubangiji yana ƙin hanyoyin mugaye, amma yana ƙaunar mutumin da yake yin abin da yake daidai.

10. Idan ka yi abin da ba daidai ba, za ka sha hukunci sosai, za ka mutu idan ka ƙi yarda da tsautawa.

11. Ko lahira ba za ta hana Ubangiji ya san abin da yake can ba. Ƙaƙa fa mutum zai iya ɓoye wa Allah tunaninsa?

12. Mai girmankai ba ya so a tsauta masa. Faufau ba zai nemi shawara a wurin masu hikima ba.

K. Mag 15