Josh 4:19-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. Rana ta goma ga watan ɗaya jama'a suka haye Urdun, suka yi zango a Gilgal a gabashin iyakar Yariko.

20. Joshuwa ya kafa duwatsun nan goma sha biyu da suka ɗauko daga Urdun a Gilgal.

21. Sai ya ce wa Isra'ilawa, “Sa'ad da wata rana 'ya'yanku suka tambayi ubanninsu ma'anar duwatsun nan,

22. sa'an nan za ku sanar da 'ya'yanku cewa Isra'ilawa sun haye Urdun da ƙafa a kan sandararriyar ƙasa!

23. Gama Ubangiji Allahnku ya sa ruwan Urdun ya ƙafe, har kuka haye kamar yadda Ubangiji Allahnku ya sa Bahar Maliya ta ƙafe har muka haye,

24. domin dukan mutanen duniya su sani Ubangiji yana da iko, domin kuma ku kasance da tsoron Ubangiji Allahnku har abada.”

Josh 4