20. Idan kun rabu da Ubangiji, kun bauta wa gumaka, sai ya juyo ya wulakanta ku, ya hallaka ku, ko da yake ya riga ya nuna muku alheri.”
21. Jama'a kuwa suka ce wa Joshuwa, “A'a, mu dai za mu bauta wa Ubangiji ne.”
22. Joshuwa kuma ya ce wa mutanen, “Ku ne shaidun kanku da kanku, kun zaɓi Ubangiji don ku bauta masa.”Sai suka ce, “I, mu ne shaidu.”
23. Joshuwa ya ce, “To, ku kawar da gumakan da suke cikinku, ku sa zuciyarku ga Ubangiji, Allah na Isra'ila.”
24. Jama'a suka ce wa Joshuwa, “Za mu bauta wa Ubangiji Allahnmu, za mu kuma yi biyayya da muryarsa.”
25. A wannan rana, Joshuwa ya yi alkawari da jama'a a Shekem, ya kafa musu dokoki da ka'idodi.
26. Ya kuwa rubuta waɗannan kalmomi a littafin Shari'ar Ubangiji. Ya kuma ɗauki wani babban dutse, ya kafa a ƙarƙashin itacen oak a wuri mai tsarki na Ubangiji.