Josh 17:14-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Kabilan Yusufu suka ce wa Joshuwa, “Me ya sa ka ba mu rabon gādo guda ɗaya? Ga shi kuwa, muna da jama'a mai yawa, gama Ubangiji ya sa mana albarka.”

15. Joshuwa kuwa ya amsa musu, ya ce, “Idan ku babbar jama'a ce, har ƙasar tuddai ta Ifraimu ta kāsa muku, to, sai ku shiga jeji ku sheme wa kanku wuri a ƙasar Ferizziyawa da ta Refayawa.”

16. Sai mutanen kabilan Yusufu suka ce, “Ƙasar tuddai ba ta ishe mu ba, ga kuma Kan'aniyawa da suke zaune a filin, da waɗanda suke a Bet-sheyan da ƙauyukanta, da waɗanda suke cikin Kwarin Yezreyel suna da karusan ƙarfe.”

17. Joshuwa kuma ya ce wa jama'ar gidan Yusufu, wato kabilar Ifraimu da ta Manassa, “Ku babbar jama'a ce, ga shi kuma, kuna da ƙarfi, ba kashi ɗaya kaɗai za ku samu ba,

18. amma ƙasar tuddai kuma za ta zama taku, ko da yake jeji ne. Sai ku sheme, ku mallaka duka. Gama za ku kori Kan'aniyawa, ko da yake su ƙarfafa ne, suna kuma da karusan ƙarfe.”

Josh 17