21. Waɗannan duka su ne birane na kan tudu, da dukan masarautar Sihon, Sarkin Amoriyawa wanda ya sarauci Heshbon. Musa ya ci shi da yaƙi da shugabannin Madayana, wato Ewi, da Rekem, da Zur, da Hur, da Reba, wato sarakunan Sihon, waɗanda suka zauna a ƙasar.
22. Jama'ar Isra'ila kuma suka kashe Bal'amu matsubbaci, ɗan Beyor, da takobi.
23. Urdun kuwa ya zama iyakar yankin ƙasar jama'ar Ra'ubainu. Wannan shi ne gādon Ra'ubainawa bisa ga iyalansu, da biranensu da ƙauyukansu.
24. Musa kuma ya ba Gadawa gādo bisa ga iyalansu.
25. Yankin ƙasarsu shi ne Yazar, da dukan biranen Gileyad da rabin ƙasar Ammonawa zuwa Arower wadda take gabas da Rabba,
26. daga Heshbon zuwa Ramat-mizfe, da Betonim, daga Mahanayim zuwa karkarar Debir,
27. da a kwarin Ber-aram, da Betnimra, da Sukkot, da Zafon, da kuma ragowar mulkin Sihon, Sarkin Heshbon. Kogin Urdun ne iyakar yankin ƙasarsu har zuwa wutsiyar Tekun Kinneret, a gabashin hayin Urdun.
28. Wannan shi ne yankin ƙasar, haɗe da garuruwa, da ƙauyuka, da aka ba mutanen kabilar Gad bisa ga iyalansu.