1. Da Adonizedek, Sarkin Urushalima, ya ji yadda Joshuwa ya ci Ai, har ya hallakar da ita sarai kamar yadda ya yi wa Yariko da sarkinta, da kuma yadda mazaunan Gibeyon suka yi amana da Isra'ilawa, har suna zama cikinsu.
2. sai ya tsorata ƙwarai, gama Gibeyon babban birni ce kamar ɗaya daga cikin alkaryai, har ma ta fi Ai girma, mazajenta duka kuwa ƙarfafa ne.
3. Adonizedek Sarkin Urushalima, ya aika zuwa ga Hoham Sarkin Hebron, da Firam Sarkin Yarmut, da Yafiya Sarkin Lakish, da Debir Sarkin Eglon, ya ce,
4. “Ku zo, ku taimake ni, mu yaƙi Gibeyon, gama ta yi amana da Joshuwa da Isra'ilawa.”
5. Sarakunan nan biyar na Amoriyawa, wato Sarkin Urushalima, da Sarkin Hebron, da Sarkin Yarmut, da Sarkin Lakish, da Sarkin Eglon, suka tattaru da dukan rundunansu, suka haura, suka kafa wa Gibeyon sansani don su yaƙe ta.
6. Gibeyonawa dai suka aika zuwa wurin Joshuwa a zango cikin Gilgal cewa, “Kada ka yar da bayinka. Ka zo wurinmu da sauri, ka cece mu, ka taimake mu, gama dukan sarakunan Amoriyawa da suke zaune a ƙasar tuddai sun tattaru a kanmu.”
7. Sai Joshuwa ya tashi daga Gilgal da dukan mayaƙa, da dukan jarumawa tare da shi.
8. Ubangiji kuwa ya ce wa Joshuwa, “Kada ka ji tsoronsu gama na riga na ba da su a hannunka, ba mutuminsu da zai iya tsayawa a gabanka.”
9. Sai Joshuwa ya tafi ya auka musu ba labari, gama daga Gilgal ya bi dare zuwa can.