5. Ku kasa kunne ga abin da Ubangiji yake faɗa, ku da kuke tsoronsa gama ya ce, “Domin kuna da aminci gare ni, waɗansu daga 'yan'uwanku suka ƙi ku, har ba su da hulɗar kome da ku. Suna yi muku ba'a suna cewa, ‘Muna so mu ga kuna murna, saboda haka bari a ɗaukaka Ubangiji.’ Amma su za su sha kunya!
6. Ku kasa kunne! Waccan babbar hayaniya cikin birni, wancan amo a Haikali, amon Ubangiji ne da yake hukunta abokan gābansa!
7. “Tsattsarkan birnina yana kama da uwa wadda ta haifi ɗa, ba tare da naƙuda ba.
8. Ko akwai wanda ya taɓa gani ko ya ji labari irin wannan abu? Ko an taɓa haihuwar al'umma rana ɗaya? Sihiyona ba za ta sha wahala ba kafin a haifi al'umma.
9. Kada ku zaci zan kawo jama'ata a wurin haihuwa in kuma hana ta haihuwa.” Ubangiji ne ya faɗa.
10. Ku yi murna tare da UrushalimaKu yi farin ciki tare da ita,Dukanku da kuke ƙaunar birnin nan!Ku yi murna tare da ita yanzu,Dukanku da kuka yi makoki dominta!
11. Za ku ji daɗin wadatarta,Kamar yaro a ƙirjin mamarsa.
12. Ubangiji ya ce, “Zan kawo muku wadata madawwamiya, dukiyar al'ummai za ta malalo zuwa gare ku kamar kogi wanda ba ya ƙafewa. Za ku zama kamar yaro wanda mahaifiyarsa take renonsa, tana rungume da shi da ƙauna.
13. Zan ta'azantar da ku a Urushalima, kamar yadda uwa take ta'azantar da ɗanta.
14. Sa'ad da kuka ga wannan ya faru, za ku yi murna, wannan zai ba ku ƙarfi da lafiya. Sa'an nan za ku sani ni ne Ubangiji, mai taimakon masu biyayya gare ni, ina kuwa nuna fushina a kan abokan gābana.”
15. Ubangiji zai zo da wuta. Zai hau a kan fikafikan hadiri, domin ya hukunta waɗanda yake fushi da su.
16. Zai hukunta dukan mutanen duniya da wuta da takobi, waɗanda ya same su da laifi, za su kuwa mutu.