1. Zan yi magana domin in ƙarfafa Urushalima,Ba zan yi shiru ba,Sai na ga adalcinta ya bayyana kamar haske,Cetonta kuma ya haskaka kamar fitila da dare.
2. Ya Urushalima, al'ummai za su ganki mai gaskiya!Dukan sarakunansu za su ga darajarki.Za a kira ki da sabon suna,Sunan da Ubangiji ya bayar da kansa.
3. Za ki zama kamar kyakkyawan rawani ga Ubangiji,Wato kambin sarauta mai daraja gare shi.
4. Ba za a ƙara ce da ke, “Yasasshiya” ba,Ko a ce da ƙasarki, “Mata wadda Mijinta ya Rabu da Ita.”Sabon sunanki yanzu shi ne, “Wadda Allah ya Yarda da Ita.”Ƙasarki kuwa za a ce da ita, “Ta yi Aure da Farin Ciki,”Domin Ubangiji ya ji daɗinki,Zai kuwa zama kamar miji ga ƙasarki.