1. Duba, ikon Ubangiji bai kasa ba, har da ba zai yi ceto ba. Shi ba kurma ba, har da ba zai ji ba.
2. Amma laifofinku suka raba tsakaninku da Allahnku. Zunubanku ne kuma suka sa ya juya daga gare ku don kada ya ji ku.
3. Gama hannuwanku sun ƙazantu da jini, yatsotsinku kuma sun ƙazantu da mugunta, leɓunanku kuma suna faɗar ƙarairayi, harsunanku kuwa suna raɗar mugunta.