Ish 57:15-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Gama haka wanda yake can Sama, Maɗaukaki, wanda ake kira Mai Tsarki ya ce, “Ina zaune a can Sama a tsattsarkan wuri, tare kuma da wanda yake da halin tuba mai tawali'u, don in farfaɗo da ruhun masu tawali'u, in kuma farfaɗo da zukatan masu tuba.

16. Ba zan yi ta gāba da ku, ko in yi ta fushi da ku har abada ba. Gama ruhu zai yi suma a gabana, da numfashin su waɗanda na halitta.

17. Na yi fushi da su saboda muguntar kwaɗayinsu, don haka na buge su. Na ɓoye fuskata, na yi fushi. Amma sun yi taurinkai, sun yi ta komawa da baya, sun bi son zuciyarsu.

18. “Na ga al'amuransu, amma zan warkar da su, zan bi da su, in ta'azantar da su tare da masu makoki.

Ish 57