Ish 54:16-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. “Ni ne na halicci maƙeriWanda ya zuga wuta ya kuwa ƙera makamai.Ni ne kuma na halicci mayaƙiWanda yakan mori makamai domin kisa.

17. Amma ba makamin da aka ƙera da ya isa ya cuce ki,Za ki iya amsa wa dukan waɗanda za su yi ƙararki.Zan kāre bayina,In kuwa ba su nasara.”Ubangiji ne ya faɗa.

Ish 54