9. Ubangiji kansa zai kāre ni,Wa zai iya tabbatar da ni mai laifi ne?Dukan waɗanda suke sarana za su shuɗe,Za su shuɗe kamar tufar da asu ya cinye!
10. Ku duka da kuke tsoron Ubangiji,Kuna kuma biyayya da kalmomin bawansa,Zai yiwu hanyar da kuke bi ta yi duhu ƙwarai,Amma ku dogara ga Ubangiji, ku jingina ga Allahnku.
11. Dukanku da kuke ƙulle-ƙullen hallaka junaƘulle-ƙullenku za su hallaka ku!Ubangiji kansa zai sa wannan ya faru,Za ku gamu da mummunar ƙaddara.