21. Su ne mutanen da na yi domin kaina,Za su raira yabbaina!”
22. Ubangiji ya ce,“Amma ba ni kuka yi wa sujada ba,Kun gaji da ni, ya Isra'ila.
23. Ba ku kawo mini hadayun ƙonawa na tumaki ba,Ba ni kuke girmamawa da hadayunku ba.Ban nawaita muku da neman hadayu ba,Ko in gajiyar da ku da roƙon turare.
24. Ba ku sayi turare domina ba,Ko ku gamshe ni da kitsen dabbobinku.Maimakon haka, sai kuka nawaita mini da zunubanku,Kuka gajiyar da ni da abubuwan da kuke aikatawa da ba daidai ba.
25. Duk da haka, ni ne Allah wanda ya shafe zunubanku,Na kuwa yi haka saboda yadda nake.Ba zan ƙara tunawa da zunubanku kuma ba.