3. Lokacin da kake yaƙi dominmu, al'ummai sukan gudu daga bakin dāga.
4. Akan tsirga a bisa abubuwan da suke da su, a kwashe su ganima.
5. Ubangiji da girma yake! Yana mulki a kan kome. Zai cika Urushalima da adalci da mutunci,
6. zai kuma sa aminci cikin al'ummar. A koyaushe yakan kiyaye jama'arsa ya kuma ba su hikima da sani. Dukiyarsu mafi girma ita ce tsoron Ubangiji.
7. Mutane masu jaruntaka suna kira don a taimake su! Jakadu waɗanda suke ƙoƙarin kawo salama suna kuka mai zafi.
8. Manyan karauku suna da hatsari har ba mai iya binsu. Aka keta yarjejeniya, aka ta da sharuɗa. Ba a kuma ganin girman kowa.
9. Ƙasar na zaman banza, an gudu an bar ta. Jejin Lebanon ya bushe, kwarin Sharon mai dausayi ya zama kamar hamada, a Bashan kuma da a kan Dutsen Karmel sai ganyaye suke karkaɗewa daga itatuwa.
10. Ubangiji ya ce wa al'ummai, “Yanzu zan tashi! Zan nuna irin ikon da nake da shi.
11. Kuka yi shirye-shiryen banza, kowane abu da kuke yi kuma ba shi da amfani. Kuna hallakar da kanku!
12. Za ku marmashe kamar duwatsun da aka ƙona don a yi farar ƙasa, kamar ƙayayuwan da aka ƙone suka zama toka.
13. Bari kowa da yake kusa da na nesa ya ji abin da na yi, ya kuma san ikona.”
14. Jama'ar Sihiyona cike da zunubi suke, suna ta rawar jiki don tsoro. Suka ce, “Hukuncin Allah kamar wuta ce mai ci har abada. Akwai wani daga cikinmu da zai iya tsira daga irin wannan wuta?”
15. Kuna iya tsira idan kuna faɗar gaskiya kuna kuma yin abin da yake daidai. Kada ku gwada ikonku don ku cuci talakawa, kada kuwa ku karɓi rashawa. Kada ku haɗa kai da masu shiri su yi kisankai, ko su aikata waɗansu mugayen abubuwa.
16. Sa'an nan za ku yi nasara, ku kuma zauna lafiya kamar kuna cikin kagara mai ƙarfi. Za ku sami abincin da za ku ci da ruwan da za ku sha.