Ish 31:5-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Kamar yadda tsuntsu yake shawagi a kan sheƙarsa don ya kiyaye 'ya'yansa, haka ni, Ubangiji Mai Runduna, zan kiyaye Urushalima in kāre ta kuma.”

6. Allah ya ce, “Jama'ar Isra'ila, kun yi mini zunubi, kuna kuwa yin gāba da ni. Amma yanzu ku komo wurina!

7. Lokaci zai yi da dukanku za ku watsar da gumakan da kuka yi na azurfa da na zinariya.

8. Assuriya za ta hallaka cikin yaƙi, amma ba ta wurin ikon mutum ba. Assuriyawa za su gudu daga bakin dāga, za a mai da majiya ƙarfinsu bayi.

9. Sarkinsu zai tsere saboda razana, shugabannin sojojinsu kuwa za su firgita, har su watsar da tutocinsu na yaƙi.” Ubangiji ne ya faɗa, Ubangiji da ake yi wa sujada a Urushalima, wanda kuma wutarsa tana ci a can domin hadayu.

Ish 31