10. Adalai za su yi murna, kome zai tafi musu daidai. Za su ji daɗin abin da suka aikata.
11. Amma mugaye sun shiga uku, za a sāka musu bisa ga abin da suka aikata.
12. Masu ba da rance da ruwa suna zaluntar jama'ata, masu ba da bashi kuwa suna cutarsu.Ya jama'ata, shugabanninku a karkace suke bi da ku, saboda haka ba ku san inda za ku nufa ba.
13. Ubangiji a shirye yake ya hurta maganarsa, a shirye yake ya hukunta al'ummai.
14. Ubangiji ya kawo dattawa da shugabannin jama'arsa a gaban shari'a. Ga laifin da ya same su da shi, “Kun washe gonakin inabi, kun cika gidajenku da abin da kuka ƙwato daga matalauta.
15. Ba ku da izinin da za ku ragargaza jama'ata, ku cuci matalauta, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.”
16. Ubangiji ya ce, “Duba irin girmankai da matan Urushalima suke da shi! Suna tafe suna hura hanci, a koyaushe suna ta fara'a irin ta yaudara, suna takawa ɗaya ɗaya a hankali da mundaye a ƙafafunsu, suna cas cas.
17. Amma zan hukunta su, in aske kawunansu, in bar su ƙwal.”
18. Rana tana zuwa sa'ad da Ubangiji zai raba matan Urushalima da dukan abin da suke taƙama da shi, da kayan adon da suke sawa a ƙafafunsu, da kawunansu, da wuyansu,
19. da hannuwansu. Zai raba su da lulluɓinsu,
20. da hulunansu. Zai raba su da layun da suke sa wa damatsansu, da kwankwasonsu,
21. da ƙawanen da suka sa a yatsotsinsu da hancinsu.
22. Ubangiji zai raba su da dukan kyawawan rigunansu na ado, da manyan rigunansu, da mayafansu, da jakunkunansu,
23. da rigunansu na yanga, da ƙyallayensu na lilin, da adikai, da gyale masu tsawo waɗanda suke sawa a kawunansu.
24. Maimakon su riƙa ƙanshin turare, za su yi wari, a maimakon abin ɗamara, za su yi ɗamara da igiyoyi masu kaushi, a maimakon su kasance da kyakkyawan gashi, za su zama masu sanƙo, a maimakon tufafi masu kyau, za su sa tsummoki, kyansu zai zama abin kunya!
25. Jama'ar garin, i, har da ƙarfafan mutane, za a kashe su a yaƙi.