Ish 24:7-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Kurangun inabi sun bushe, ruwan inabi ya yi kaɗan. Dukan wanda yake farin ciki a dā, yanzu sai baƙin ciki yake yi,

8. kaɗe-kaɗen garayunsu da gangunansu na farin ciki sun ƙare.

9. Babu sauran waƙar farin ciki ga mashayan ruwan inabi, ba kuma wanda zai ƙara jin daɗin ɗanɗanar ruwan inabi.

Ish 24