Ish 15:1-2 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Wannan shi ne jawabi a kan Mowab.Biranen Ar da Kir, an hallaka su dare ɗaya, ƙasar ta yi tsit, ba kowa.

2. Mutanen Dibon sun hau kan tuddai don su yi kuka a matsafarsu. Mutanen Mowab suna kuka da baƙin ciki saboda biranen Nebo da Medeba, sun aske kawunansu da gyammansu saboda baƙin ciki.

Ish 15