Ish 14:2-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Al'ummai da yawa za su taimaki jama'ar Isra'ila su koma ƙasarsu wadda Ubangiji ya ba su. A can sauran al'umma za su yi wa Isra'ila hidima kamar bayi. Waɗanda suka kama Isra'ilawa a dā yanzu Isra'ilawa za su kama su. Jama'ar Isra'ila za ta mallaki waɗanda suka taɓa zaluntarsu.

3. Ubangiji Allah kuwa zai sawwaƙe wa jama'ar Isra'ila azaba da wahala da suke sha, daga kuma aikin da aka tilasta su su yi.

4. Sa'ad da ya aikata wannan za su yi wa Sarkin Babila ba'a.Za su ce, “Mugun sarkin ya fāɗi, ba zai ƙara zaluntar kowa ba!

5. Ubangiji ya ƙare mulkin mugun,

6. wanda yake zaluntar jama'a a husace, bai taɓa daina tsananta wa al'ummai ba, wanda ya ci da yaƙi.

7. Yanzu magana ta ƙare, duniya duka tana jin daɗin hutawa da salama. Kowa na ta raira waƙar murna.

Ish 14