Ish 11:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Gidan sarautar Dawuda kamar itacen da aka sare ne, amma kamar yadda rassa sukan toho daga cikin kututture, haka nan za a sami sabon sarki daga zuriyar Dawuda.

2. Ikon Ubangiji zai ba shi hikima,Da sani, da gwaninta yadda zai mallaki mutanensa.Zai kuwa san nufin Ubangiji, ya kuma yi tsoronsa,

3. Zai ji daÉ—in yin hidimarsa.Ba zai yi shari'ar ganin ido ko ta waiwai ba.

Ish 11