Irm 8:20-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Mutane suna ta cewa,“Damuna ta ƙare, kaka kuma tawuce,Amma ba a cece mu ba.”

21. Raunin da aka yi wa jama'ata,Ya yi wa zuciyata rauni.Ina makoki, tsoro kuma ya kama niƙwarai.

22. Ba abin sanyayawa a Gileyad ne?Ba mai magani a can ne?Me ya sa ba a warkar da jama'ataba?

Irm 8