Irm 6:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Ya ku mutanen Biliyaminu, kugudu neman mafaka,Daga cikin Urushalima!Ku busa ƙaho a Tekowa,Ku ba da alama a Bet-akkerem,Gama masifa da babbar halaka sunfito daga arewa.

2. Ya Sihiyona, ke kyakkyawarmakiyaya ce, zan hallaka abin dakika hahhaifa.

3. Makiyaya da garkunansu za su zowurinki,Za su kafa alfarwansu kewaye da ke,Kowa zai yi kiwo a makiyayarki.

4. Za su ce, ‘Mu yi shiri mu fāɗa matada yaƙi!Ku tashi, mu fāɗa musu da tsakarrana!’Sai kuma suka ce, ‘Kaitonmu, garana tana faɗuwa, ta yi ruɗa-kuyangi.

5. Mu tashi mu fāɗa mata da dare,Mu lalatar da fādodinta.’ ”

11-12. Don haka ina cike da fushinUbangijiNa gaji da kannewa.Ubangiji ya ce,“Zan kwararo fushi kan yara da suke atiti.Da kuma kan tattaruwar samari.Za a ɗauke mata da miji duka biyu,Da tsofaffi, da waɗanda suka tsufatukub-tukub.Za a ba waɗansu gidajensu, dagonakinsu, da matansu,Gama zan nuna ikona in hukuntamazaunan ƙasar.

Irm 6