31. A shekarar da Ewil-merodak ya zama Sarkin Babila, sai ya nuna wa Yekoniya Sarkin Yahuza alheri. Ya fisshe shi daga kurkuku. Wannan ya faru ran ashirin da biyar ga watan goma sha biyu a shekara ta talatin da bakwai bayan da aka kai Yekoniya bauta.
32. Ewil-merodak ya nuna wa Yekoniya alheri, ya ba shi matsayi na daraja fiye da waɗansu sarakunan da aka kai su bautar talala a Babila tare da shi.
33. Yekoniya ya tuɓe tufafin kurkuku, ya riƙa cin abinci kullum a teburin sarki, har dukan sauran kwanakin ransa.