Irm 52:10-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Ya kuwa kashe 'ya'yan Zadakiya a idonsa. Ya kuma kashe dukan shugabannin Yahuza a Ribla.

11. Sa'an nan ya ƙwaƙule idanun Zadakiya, ya kuma sa masa ƙuƙumi, aka kai shi Babila inda aka sa shi a kurkuku har ran da ya mutu.

12. A kan rana ta goma ga watan biyar a shekara ta goma sha tara ta sarautar Nebukadnezzar, Sarkin Babila, sai Nebuzaradan shugaban matsara da kuma ɗan majalisar sarki, ya zo Urushalima.

13. Sai ya ƙone Haikalin Ubangiji, da gidan sarki, da dukan manyan gidajen da suke Urushalima.

14. Sojojin Kaldiyawa da suke tare da shugaban matsara, suka rushe dukan garun Urushalima.

15. Sa'an nan Nebuzaradan shugaban matsara ya kwashe waɗansu matalauta, da sauran mutane da aka bari a birnin, da waɗanda suka gudu zuwa wurin Sarkin Babila, da sauran masu sana'a, ya kai su bautar talala a Babila.

16. Amma ya bar waɗansu matalauta na gaske a ƙasar don su yi aiki a gonakin inabi, da sauran gonaki.

17. Kaldiyawa kuwa suka farfasa ginshiƙan tagulla, da dakalai, da babbar kwatarniya, waɗanda suke a Haikalin Ubangiji. Suka kwashe tagulla duka suka kai Babila.

Irm 52