Irm 51:40-51 Littafi Mai Tsarki (HAU)

40. Zan kai su mayanka kamar 'yanraguna, da raguna, da bunsurai.

41. “An ci Babila,Ita wadda duniya duka take yabo ancinye ta da yaƙi,Ta zama abar ƙyama ga sauranal'umma!

42. Teku ta malalo a kan Babila,Raƙuman ruwa masu hauka sunrufe ta.

43. Garuruwanta sun zama abinƙyama,Ta zama hamada, inda ba ruwa,Ƙasar da ba mazauna,Ba kuma mutumin da zai ratsa tacikinta.

44. Zan hukunta Bel, gunkin Babila,Zan sa ya yi aman abin da yahaɗiye,Ƙasashen duniya ba za su ƙarabumbuntowa wurinsa ba.Garun Babila ya rushe!”

45. “Ku fito daga cikinta, ya jama'ata,Kowa ya tsere da ransa daga zafinfushin Ubangiji.

46. Kada zuciyarku ta yi suwu,Kada kuma ku ji tsoro sabodalabarin da ake ji a ƙasar,Labari na wannan shekara dabam,na wancan kuma dabam,A kan hargitsin da yake a ƙasar,Mai mulki ya tasar wa mai mulki.

47. Saboda haka kwanaki suna zuwa,Sa'ad da zan hukunta gumakanBabila,Za a kunyatar da dukan ƙasarBabila,Dukan matattunta za su faɗi atsakiyarta.

48. Sa'an nan sama da duniya, da dukanabin da take cikinsu,Za su raira waƙar farin ciki,Domin masu hallakarwa daga arewada za su auko mata,Ni Ubangiji na faɗa.”

49. Babila za ta fāɗi,Saboda mutanen Isra'ila da dukanmutanen duniya waɗanda takashe.

50. Ku waɗanda kuka tsere wa takobi!Ku gudu! Kada ku tsaya!Ku tuna da Ubangiji a can nesa indakuke,Ku kuma yi ta tunawa daUrushalima.

51. Mun sha kunya saboda zargin da akeyi mana,Kunya ta rufe mu,Gama baƙi sun shiga tsarkakanwurare na Haikalin Ubangiji.

Irm 51