Irm 51:21-33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Da kai ne na karya doki damahayinsa,

22. Da kai ne na farfasa karusa damahayinsa.Da kai ne na kakkarya mace danamiji,Da kai ne na kakkarya tsoho dasaurayi,Da kai ne na kakkarya saurayi dabudurwa,

23. Da kai ne na kakkarya makiyayi dagarkensa,Da kai ne na kakkarya manoma dadawakan nomansa,Da kai ne na kakkarya masu mulkida shugabanni.”

24. Ubangiji ya ce, “Zan sāka wa Babila da dukan mazaunan Kaldiya a ganin idanunku saboda dukan muguntar da suka aikata a Sihiyona.

25. Ga shi, ina gaba da kai, ya dutse maihallakarwa,Wanda ya hallaka duniya duka.Zan miƙa hannuna gāba da kai,Zan mirgino da ƙasa dagaƙwanƙolin dutse,Zan maishe ka ƙonannen dutse.

26. Ba za a sami dutsen yin kusurwa, kona kafa harsashen gini a cikinkaba,Amma za ka zama marar amfani harabada.”

27. Ku ta da tuta a duniya,Ku busa wa ƙasashen duniya ƙaho,Ku shirya ƙasashe don su yi yaƙida ita,Ku kirawo mulkokin Ararat, da naMinni, da na Ashkenaz, su yi yaƙida ita.Ku naɗa sarkin yaƙi wanda zaishugabanci yaƙin da za a yi da ita,Ku kawo dawakai kamar fāra.

28. Ku shirya ƙasashe su yi yaƙi da ita,Sarakunan Mediyawa, da masumulkinsu, da shugabanninsu,Da kowace ƙasar da take ƙarƙashinmulkinsu.

29. Duniya ta girgiza, tana makyarkyatasaboda azaba,Gama nufin Ubangiji na gāba daBabila ya tabbata,Nufinsa na mai da ƙasar Babilakufai, inda ba kowa.

30. Sojojin Babila sun daina yaƙi, sunazaune a cikin kagaransu.Ƙarfinsu ya ƙare, sun zama mata,An sa wa wuraren zamanta wuta,An karya ƙyamaren ƙofofingarinta.

31. Maguji yana biye da maguji a guje,Jakada yana biye da jakada,Don su faɗa wa Sarkin Babila, cewaan ci birninsa a kowane gefe.

32. An ƙwace mashigaiAn ƙone fadamu da wuta,Sojoji sun gigice.

33. Ni Ubangiji Mai Runduna, Allah naIsra'ila na ce,“Mutanen Babila sun zama kamardaɓen masussukaA lokacin da ake sussuka,Ba kuwa da daɗewa ba lokacin girbeta zai zo.”

Irm 51